Gwamnan Jihar Birno Farfesa Babagana Umar Zulum ya bawa shugaban ma aikatar fadar gwamnatin jihar dama don bimcike kan tashin gobara a kasuwar waya.

An samu tashin gobara a babbar kasuwar waya da ke Maiduguri wanda ta cinye kayan miliyoyin kuɗaɗe, sai dai ana zargin wuntar lantarki ce tayi sanadi.

Cikin zamtawarsa da kamfanin ɗillacin labarai na ƙasa NAN Gwamna Zulum da ke ƙasar saudiyya ya ce da zarar ya dawo Najeriya zai tabbatar an gano musabbabin tashin gobarar tare da daƙile faruwar hakan a nan gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: