Connect with us

Labarai

Sabon kwamishinan ƴan sandan jihar Kano ya fara aiki a yau, kun san wanene shi?

Published

on

Abdullahi Haruna kakakin ƴan sandan jihar Kano ne ya rubuta

Ayau, sabon kwamishinan Yansanda na Jihar kano, CP Habu Ahmadu Sani, psc ya kama aiki. An haifi Kwamishinan ‘Yansanda HABU Ahmadu Sani, a gidan Sarautar dake gidan Bango ta yankin Dinbiso a Karamar Hukumar Mulki ta Wurno a Jahar Sokoto ranar 7 ga watan Afrilu 1964.

Bayan yayi nasarar kamala karatunsa na Firamare da Sakadare daga shekarar 1971 zuwa 1982. Ya zarce zuwa Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sokoto, a inda ya kamala karatun digiri na farko tare da samun shaidar digiri a fannin Ilimin kimiyyar doron kasa da sararin samaniya watau (Geography) daga shekara ta 1985-1990.

Daga nan ne kuma gwamnatin tarayyar Nigeria ta turashi aikin bautawa kasa (NYSC) a tsohuwar jahar Gongola (Jihar Adamawa a yanzu) daga shekara ta 1990 -1991, a inda yakoyar a makarantar sakandare dake karamar hukumar Ganye.

Kwamishinan ‘Yansanda Abubakar (Habu) Ahmadu Sani, yasamu dammar shiga aikin Rundunar ‘Yansandan Najeriya (Nigeria Police Force) a mukamin mataimakin sufuritandan ‘Yansanda (Cadet ASP) a watan Mayu na shekara ta 1990, ya kuma samu horo na aikin Dansanda a makarantar horas da manyan jami’an ‘Yansanda dake Kaduna (Police Academy Annex Kaduna).

Tundagawannanlokacin ne kumayafararikematsayidabandaban a Rundunar ‘Yansandan Nigeria a nan gida Nigeria da kumakasashenwaje.

A lokacin da yake tasowa da mukamai na matsakaicin Dansanda (ASP-CSP), yarika matsayi da damana Baturen Dansanda me kula da yanki wato (DPO) da kuma jami’in kula da sashen tattarawa da samar da bayanan sirri na Rundunar ‘Yansandan Nigeria a jihohi da dama dake kasarnan, wadanda sukahada da Jihohin Jigawa, Kebbi, Cross River da Niger da kuma aiki a manyan ofisoshin ‘Yansanda kamarsu offishin ‘Yansanda me kula da tashar jirgin ruwa a Lagos, offishin gudanar da aikin mulki dake yanki na shida (Zone 6 Calabar), jami’in aiwatarwa a makarantar horaswa kansamar da bayanen sirri ta ‘Yansanda dake Jihar Enugu.

Ya kumayi aiki da rundunar samadda zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sudan ta Kudu a matsayin jami’i me tsarawa da shiryawa da kuma horaswa ga jami’an ‘Yansanda dake Jihar Unity mai helkwata a garin Bentiu a kasar Sudan ta Kudu.

Yayin da Allah yakaishi matsayin matemakin Kwamishinan ‘Yansanda, Rundunar ‘Yansanda Najeriya ta turashi aiki a rundunar ‘Yansanda dake Jihar Niger a matsayin mataimakin Kwamishinan ’Yansanda maikula da sashen binciken manyan laifuka da kuma tattara bayanan sirri. Daganan ne kuma, sakamakon basirarsa da sadaukar da kai ga aikin samar da tsaro, kare lafiya da dukiyoyin al’umma, Rundunar ‘Yansanda ta Kasa ta mayar dashi babban helikwatar ta dake Abuja don kula da sashen tattarawa tare da samar da bayanan sirri dake amfani da na’urori na zamani, tare da kara masa matsayi zuwa ga mukamin Mukaddashin Kwaminishin ‘Yansanda.

Hakazalika saboda hazakarsa da kuma nasarorin da yasamarwa da Rundunar wajan dakile tare da kama manyan masu laifuffuka a cikin kasarnan, Rundunar ta turashi zuwa ofis da yake aiki kai tsaye karkashin babban Sifeto Janar na ‘Yansandan Najeriya domin ya shugabanci sashen kula da bincike da sa’ido a ayyukan ‘Yansanda na Najeriya, kana kuma ta kara masa girma zuwa Kwamishinan ‘Yansanda.

A lokacin da yake wannan ofishi, yanakula, tsarawa da kuma jagorantar kwararrun ‘Yansanda namusamman masu bincike da kuma yaki da miyagun laifuka kamarsu, Sahen Binkicen Sirri da Ayyukan Gaggawa wanda kekar kashinSifetoJanar na ‘Yansanda (IGP Intelligence Response Team), Runduna ta Musamman Masu DabarunYaki Akan Miyagun Laifuka (Special Tactical Squad) Cibiyar Bincike KanYaki da AyyukanTa’addanci (Terrorism Investigation Burea), Cibiyar Nazari, Bin Kwakwafi Tare da Kama Masu Aikata Laifuka (Analytical Tracking and Interception Center) da sauran manyan ayyuka na bincike da gudanar da mulki wanda Babban Sifeton ‘Yansanda yake bashi a wancan lokaci.

Kafin turashi don shugabantar Rundunar ‘Yansanda dake Jahar Bauchi, shine Kwamishinan ‘Yansanda maikula da sashen samar da bayanan sirri a helikwatar ‘Yansanda dake Abuja kuma adaidai wancan lokacin shine mataimaki me kula da bangaren samar da bayanan sirri, a sabon salon yaki da aikata manyan laifuka, mai taken PUFF-ADDER wanda badadadewa bane Sifeto Janar na ‘Yansanda nakasa Mohammed AbubakarAdamu NPM, mni, yakaddamar dashi domin yaki da miyagun laifuffuka a kasannan.

Kwamishina HABU Ahmadu yakama ragamar shugabancin Rundunar ‘Yansanda ta Jahar Kano ranar ashirin gawatan Nuwamba shekara ta 2019, kujerar da yake kai har zuwa yanzu.

KWASAKWASAI, BITOCI DA KUMA SAMINONI DA YA HALARTA

Kwamishinan ‘Yan Sanda Abubakar Ahmadu, yasamu halartar kwasa-kwassai da dama da taron karawa juna sani da saminoni anan gida Nigeria da kuma kasashen waje, daga cikinsu akwai haka:-

1. Yasamu horo akan tsare-tsare a Makarantar horas da manyan hafsoshin ‘Yansanda dake Jos.
2. Yasamu horo akan shugabanci na matsakaitan hafsoshin ‘Yansanda a makarantar manyan hafsoshin ‘Yansanda dake Jos.
3. Yasamu horo akan kwarewa kansamar da bayanan sirri a Makarantar horas da jami’an sojojin Najeriya a fannin tattarawa da samar da bayanan sirri dakeTego, Lagos.
4. Yayi Kwas na kwararru a bangaren sarrafa bayanan sirri.
5.Yayi Kwas akan gano takar dunboge da harkokin tsaro na iyakokin kasashe a Cesena dake KasarItaliya.
6.Haka kuma ya halarci wasu kwasa-kwasai a cibiyar horaswa da kuma binciken bayanai ta Majalisar Dinkin Duniya kamar haka:-
i. Ta addanci a fadin duniya
ii. Dokar Kasa da Kasa kan ‘Yancin Dan’adam da kuma dokokin yake-yake wanda ake amfani da makamai.
iii. Nazari kan abubuwa masu fashewa, da yadda suke shafar Dan’adam tare da samar da agaji, fasahar dake tattare dasu da kuma yadda za’a magancesu.

Kwamishinan ‘Yan Sanda Abubakar Ahmadu yakasance wakili ne na kungiyoyin kwararru da masana a fannin ilimi da shugabanci kamar haka:-

Wakili a cibiyar gudanar da hada-hada tsakanin gwamnati da kuma rukunoni masu zaman kansu.

TAKARDUN KARRAMAWA DA KUMA LAMBOBIN YABO GA KWAMISHINAN ‘YANSANDA

HABU Ahmadu yakarbi takardun yabo da dama anan cikin gida da kuma wajen Nigeria domin hazakar sa da kuma kwazo wajen aikinsa.
Wadannan takardun sun hada da:
1. Ya samu lambar yabo ta kwazon aiki daga Majalisar Dinkin Duniya sakamakon gudunmawarsa wajen kawo zaman lafiya a Sudan ta Kudu.
2. Ya samu lambar yabodaga Kwamishinan ‘Yansanda na Majilisar Dinkin Duniya sakamakon koyar da ‘Yansandan Bentiu dake kasar Sudan ta Kudu.
3. Ya samu takardar yabo daga Mataimakin Sifeta Janar na ‘Yansanda kan sadaukar da kai, tsayuwar daka akan aiki da kuma kwarewa wajen bayar da rahoto a kuma akan lokacin da ya dace.
4. YasamuTakardar yabo daga mataimakin Sifeta Janar ‘Yansandan Nigeria kan gudanar da aiikin tsaro da ya cancanci yabo daga Rundunar ‘Yansandan.
5. Ya samu takardar yabo kan kasancewa Baturen Dansanda da yafi kowa hazaka da kwazo a shekarar 2001 a JiharJigawa.

Kwararre kuma nagartaccen Jami’in Dansanda wanda yasamarwa da Rundunar ‘Yansandar Nigeria nasarori a baya kuma yake kan samarwa, Kwamishinan ‘Yansanda HABU Ahmadu Sani, yatsara tare da jagorantar ayyukan ‘Yanda da akayi amfani da bayanan sirri da dama wanda yayi sanadiyar kame manya-manyan ‘Yan ta’adda da kuma kwato bindigogi, da albarusai da sauran muggan makamai masu dinbin yawa.

Kwamishinan ‘Yansanda HABU Ahmadu Sani, yana da Aure kuma Allah ya Albarkaceshi da ‘Ya ‘ya maza da mata.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Sama Da Mutane 85 cikin 100 Na Amfana Da Tallafin Wutar Lantarki

Published

on

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya yi magana kan janye tallafin wutar lantarki da gwamnatin tarayya ta yi.

 

Ministan ya ce sama da Naira tiriliyan 1 da za a samu sakamakon janye tallafin wutar lantarki, za a yi amfani da su wajen inganta samar wutar lantarki da ayyukan more rayuwa a ƙasar nan.

 

Jaridar The Nation ta ce Idris ya bayyana haka ne a Kaduna a jiya lokacin da ake tattaunawa da shi a shirin ‘Hannu da Yawa’ na Rediyo Najeriya da ke Kaduna.

 

Ministan ya ce wasu ƴan tsiraru masu hannu da shuni da kamfanoni ne kawai ke kwashe garaɓasar tallafin wutar lantarkin.

 

A cewarsa kaso 40% na tallafin wutar lantarkin yana amfanar kaso 15% da ke samun wutar lantarki ta sa’o’i 20 a kowace rana.

 

Idris ya jaddada cewa har yanzu kaso 85% cikin 100% na al’ummar da suke ƙarƙashin sauran rukunonin wutar lantarkin na samun tallafi.

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Kano Ya Nuna Bacin Rai Kan Sakin Yan Daba A Kano

Published

on

Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya nuna bacin ransa kan yadda aka saki ‘yan daba da ke kulle a jihar.

Gwamnan ya ce wannan wani mataki ne na kawo tsaiko a kokarin da gwamnati ke yi na dakile matsalar dabanci a jihar.

Abba Kabir ya bayyana haka ne yayin tarbar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan gwamnati.

Ya bayyana yawan ‘yan dabar da aka kama domin yi musu hukunci amma abin takaici an sako su.

Har ila yau, gwamnan ya zargi jam’iyyun adawa da kokarin kubutar da ‘yan dabar domin biyan buƙatar kansu ta siyasa.

Continue Reading

Labarai

Jagororin APC A Ondo Sun Zargi Gwamnan Jihar Da Yin Makarkashiya A Zaben Fidda Gwani

Published

on

Wasu jagororin jam’iyyar APC a Jihar Ondo sun zargi gwamnan Jihar Lucky Ayedatiwa akan kulla makarkashiya akan zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar wanda za a gudanar a ranar 20 ga watan Afrilu da muke ciki.

 

 

 

Jagororin jam’iyyar karkashin wata kungiya mai rajin tabbatar da shugaban nagari a Jihar sun ce gwamnan na kokari sauya zaben na fidda gwani.

 

 

 

Shugaban kungiyar Evangelist Tade Ojo ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya aikewa da shugaban kasa Bola Tinubu kan lamarin.

 

 

 

Shugaban ya ce gwamnan tare da magoya bayansa sun buga katuna da tambarin jam’iyyar su na rabawa mutanen da ba mambobin jam’iyyar ba.

 

 

 

Shugaban ya bukaci jam’iyyar APC ta kasa da shugaban kasa Tinubu da su dakatar da Ayedatiwa akan yunkurin tarwatsa zaben na fidda gwani.

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: