Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Habu Ahmadu Sani ya tabbatar da cewar rundunar ƴan sandan jihar Kano za ta bada goyon baya don wayar da kan al’umma dangane da shaye shaye.

A yayin da shugabancin ɓangarori daban daban suka kaiwa kwamishinan wata ziyarar maraba, ƙungiyar masu shirya fina finai ta Kano Kannywood sun karrama kwamishinan kasancewarsa mai faɗa da cikawa.

Yayin da yake jawabi shugaban jarumai a masana antar Alaan Kwalle ya roƙi rundunar ƴan sanda da su haɗa kai ƴan masan antar don wayar da kan al umma.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Habu Ahmadu ya sha alwashin ba da dukkanin goyon baya don tallafawa masana antar ta ci gaba musamman ɓangaren masu satar fasaha.
Mujallar Matashiya ta gano manyan Jarumai daban daban da halarci taron ciki har da wasu daga cikin masu ba da umarni.