Wata babbar kotu dake zaune a Garin Abakaliki jihar Ebonyi ta yanke wa wata mata hukuncin kisa ta hanyar Rataya.

Matar Mai suna Agnes Nweferu kotu ta kamata ne da laifin kashe kishiyarta Mai suna Felicia da Yayanta 7 ta hanyar cinna wa bangarenta wuta.
Yan sandan da suka gabatar da karar sun bayyana cewa bincike ya tabbatar da cewa sai da ta kwashe Yayanta daga gidan kafin kafin ta cinna wa gidan wuta.

