Rundunar yan sandan jihar oyo ta yi holen mutane 18 da ake zargi da aikata laifukan da suka hadar da fashi da makami, garkuwa da mutane, cikin mutanen da aka kama akwai wani Gbenga Oduola da ke hayar babur wato achaba ake zargin ya hallaka wani yaro mai shekaru 5 tare da yiwa mahaifiyar yaron fyade.

Wanda ake zargin ya bayyana cewar ya dauki matar ne a babur dinsa sai yake fada mata cewar yana sonta hakan ya sa ta amince kuma ya kaita gidansa har ya mata fyade.
Ya cigaba da cewar ya kashe dan matar ne saboda baya son abinda zai kawo masa cikas tsakaninsa da matar, ya kuma binne kan yaron a shagonsa sannan ya jefar da ganganr jikinsa a cikin daji, amma yaron bai aikata masa laifin komai ba, sannan bai taba kashe kowa ba a rayuwarsa.

Kwamishinan yan sandan jihar Shina Olukolu ne ya gabatar da wanda ake zargin a gaban yan jaridu, yace lamarin ya faru ne a ranar 9 ga watan disamban da muke ciki.
Kwamishinan yace sun yi nasarar samun gangar jikin yaron da aka kasha kuma sun mika zuwa babban asibiti don gudanar da bincike
