Fadar Shugaban kasar Najeriya ta fitar da wata sanarwar da ke nesanta shugaba Muhammadu Buhari da hannu wajen gabatar da kudirin da ke shirin mayar da tsarin kowanne wa’adi na mulkin kasar zuwa shekaru 6.

sanarwar da fadar Shugaban kasar Najeriya ta fitar ta bayyana cewa bata goyon bayan wani dan Majalisar wakilai mai suna Mr John Dyegh da ya gabatarwa Majalisar kudi
Sanarwar da babban mataimaki na musamman ga shugaba kasa Muhammadu Buhari kan al’amuran da suka shafi Majalisa Senator Babajide Omoworare, ya bayyana cewa shugaban Najeriyar ya sha nanata rashin bukatar shi ta kara koda kwana guda a mulki bayan karewar wa’adinsa, hasalima ya sha alwashin kin mara baya ga kowanne dan siyasa yayin zaben shekarar 2023.

Don haka wannan kudiri da dam majalisa ya nema bada sa hannun fadar Shugaban kasa bane Kuma basa goyon bayan hakan a cewar Babajide.
