Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano kuma babban na hannun daman Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wato Rabiu Suleiman Bichi ya canja sheka zuwa jam’iyyar APC.
Rabi’u Bichi dai ya sauya shekar ne biyo bayan yanke hukuncin shari’ar gwamnan Kano da kotun koli ta yi, inda ta tabbatarwa da Ganduje kujerar Gwamnan Kano.
Haka kuma rahotanni sun nuna cewa dubban wasu magoya bayan PDP a Kano na shirin komawa tafiyar Gandujiyya bayan shan kayi da suka yi a Kotun Koli.

Leave a Reply

%d bloggers like this: