Rahotannin da muke samu yanzu Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kama wasu malamai biyu.

sakamakon bijirewa umarninta na hana Sallar Juma’a a jihar.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar,
Inda ya bayyana cewa malaman da aka kama sun hada da Malam Aminu Umar Usman,
da kuma Malam Umar Shangei wadanda aka kama a Malali da Unguwar Kanawa.

Aruwan Ya bayyana cewa abin da malaman suka yi ya sabawa dokar jihar ne da kuma umarnin da manyan malamai suka bayar.
Dan haka za su fuskanci hukuncidai-dai da laifin su.

Majiyarmu ta Muryar yanci ta rawaito cewa,
Aruwan ya bayyana cewar gwamnatin jihar ba zata yi kasa a gwuiwa ba wurin ganin ta hukunta duk wani Wanda ya karya dokar da gwamnatin ta gindaya a fadin jihar.
Wannnan doka na yin sallar juma’a ya biyo bayan matakan da Gwamnatin ke dauka na dakile yaduwar Cutar Corona Virus.