A sakamakon gwajin da aka yiwa uwargidan gwamnan Kano Hajiya Hafsat Abdullahi Gamduje da mai gidanta Abdullahi Umar Ganduje an tabbatar da cewar ba sa ɗauke da cutar Covid~19.
Cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan kano Mallam Abba Anwar ya fitar, sanarwar ta ce gwamnan ya roƙi jama ar jihar Kano da su cigaba da kiyaye hanyoyin da za su kare kansu daga kamuwa da cutar.
Ya ƙara da nuna godiya ga jami an hukumar da aka kafa don yaƙi da cutar a Kano don ganin an ɗaƙile ɓulla da yaɗuwar cutar baki ɗaya.
Sannan yayi godiya ga Allah da ya kare jihar Kano daga ɓullar cutar a jihar.