Daga Maryam Muhammmad

Kwamitin yaki da cutar c
Corona hadin gwiwa da gwamnatin kano sun shirya wata bitar kwana guda ga ‘yan jaridun jihar domin sanin hanyoyi dabarun kare kai daga kamuwa da cutar k
Corona.
Kwamishinan yada labarai na jihar kano Malam Muhammadu Garba shine ya sanar da hakan a cikin wata takarda da ya fitar, inda yace za’a bada horon ne ga ‘yan jarida 100 na gidajen radio da talabijin da mujalla a matakin jiha da kasa wanda ake sa ran farawa a yau Asabar a babban dakin taro na coronation hall dake gidan gwamnatin kano.

Ya kuma ce za’a sanar da yan jaridu bukatar dake akwai na tabbatar da ganin sun samu horon bayar da kariya yayin tafikar da aiyukansu na yau da kullum kasancewarsu fitilar dake haskaka duniya.

Malam Garba ya shaida cewa gwamnatin Kano ta damu matuka akan yadda ‘yanjarida za su samu cikakkiyar kariya a yayin da suke aikin hidimtawa al’umma da sanar dasu halin da duniya ke ciki ba tare da sun hadu da wata matsala ba.
A yayin bitar dai za’a gabatar kasida kan yaki da cutar corona a aikin jarida.
Takardar kasidar ta kunshi kasida a hanyoyin sadarwa wanda Dr Sani Gwarzo zai gabatar, da kariya daga corona a kafofin sadarwa, da wata kasidar akan yada labarai kan macece corona da yadda ake kamuwa da ita da kuma hanyoyin maganceta.