Gwamnatin Jihar Kaduna ta koro Almajirai dubu 35 zuwa jihohi daban daban dake makwabtaka da jihar.

Kwamishiniyar Jin kai da Inganta Rayuwar Al’umma ta Jihar, Hajiya Hafsat Baba ce ta sanar da hakan ga manema labarai.

Kwamishiniyar ta ce, wannan matakin da aka dauka, na cikin yunkurin gwamnatin jihar na tabbatar da cewa, dukkanin kananan yara sun samu ilimin Al-Kur’ani da na zamani karkashin kulawar iyayensu.

Hajiya Hafsat ta ce, Ma’aikatarta tare da agajin Asusun Tallafa wa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, na kula da Almajiran da wasu jihohin suka turo su zuwa Kaduna.

Kwamishiniyar ta ce, wasu daga cikin Almajiran na fama da wasu nau’ukan cutuka da ke bukatar kulawa ta musamman.

Madogara

Leave a Reply

%d bloggers like this: