Babban alkalin jihar Kogi Mai Shari’a Nasir Aljannah ya rasu sakamakon Cutar Corona.

Rahotanni dai sun bayyana cewa Mai Shari’a Nasir ya rasu ne a safiyar yau Lahadi a cibiyar killacesu masu dauke da Cutar Corona dake garin gwagwalada a birnin Abuja.

Kamar yadda daya Daga cikin Iyalan gidansa ya tabbatar da Mutuwar a safiyar yau.

Mutuwar tasa tazo ne kasa da makonni biyu da Mutuwar wani jami’in tsaron Gwamna Yahya Bello a wani Asibiti dake Abuja Wanda ake zaton Shima ya mutu ne sanadin Cutar Corona.

Madogara TheCable

Leave a Reply

%d bloggers like this: