Gwamnan Kano Dr Abdullahi umar ganduje ya gargadi yan kasuwar Sabon gari masu saida magunguna dasu koma kasuwar dangwauro.

Gwamnan yayi wannan Kira ne biyo bayan jagorantar Kona wasu jabun magunguna da ya kai kimanin Naira Miliyan 380 Wanda hukumar dake yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi Ta kasa Reshen jihar NDLEA ta kama.
Wannan dai bashi bane Karo na farko da gwamnatin jihar Kano take bawa yan Kasuwar magunguna dake sabon Gari umarnin komawa sabon kasuwa da aka Gina dake Dan gwauro.

Ganduje ya kuma bayyana cewa wannan umarnin daga gwamnatin tarayya ne cewa a bude kasuwar magunguna wajen daya.

Gwamnan dai yayi Kira da kakkausan murya akan komawa kasuwar dangwauro inda yace duk wani dan kasuwa dake da korafi game da sabon kasuwar to ya kai korafin ofishinsa kai tsaye inda zai Kira masu fada aji don magance matsalar