Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wata mata mai suna Zahira Shu aibu bisa zargin kwarawa mijinta ruwan zafi a jikinta har ya ƙone.

Mai magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kama matar ne wanda ake zargi bayan faɗa ya kaure tsakaninsu wanda mijin ya daketa ita kuwa ta kwara masa ruwan zafi har ya ƙona cikinsa, cinyoyinsa da ƙafarsa

Tuni aka garzaya da su babbar helkwatar da ke unguwar bompai don ciggaba da bincike.

Mijin mai suna Abdulmitallib Gambo ya bayyana cewar, ya bawa matar tasa umarni da ta yi musu girki sai ta ce tana binsa bashin kuɗin cefane kuma bai biya ba, wannan ne sanadin da suka samu saɓani.

Matar mai suna Zahira ta amsa cewa tabbas ta watsawa mijin nata ruwan zafi amma ta musanta batun saransa da adda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: