Kungiyar matasan Kano kungiya ce da aka kirkireta don gwagwarmayar Kwato wa matasa hakkokinsu da ake danne musu daga wasu Ma’aikatu masu zaman kansu da bankuna, sauran ma’aikatu.

Kungiyar Karkashin Jagorancin kwamared Alhassan Haruna Dambatta dake da Wakilai a Kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

A yau ne dai kungiyar ta kaddamar da Taken kungiyar a Karamar Hukumar Dambatta.

Taken da suka yi wa kungiyar Shine (kungiyar Matasan Kano- Gwagwarmaya- Yanci). Wanda Dr Kabiru Sa’id Sufi ya kaddamar A Islamic Center dake Garin Dambatta.

Da yake jawabi shugaban kungiyar Alhassan Haruna Dambatta ya ce Babbar manufar wannan kungiya shine gwagwarmayar Kwato wa matasa hakkokinsu, kuma kungiyar a shirye take wajen shigewa, matasa gaba akan duk wani hakki da aka danne musu ta hanyar da doka ta tanadar.

A cewarsa akwai hakkoki na kamfanunuwa da zasu rika saukewa wajen matasan jiha ko yanki kamar yadda doka ta tanadar amma basa yi.

Ya kara da cewa ragowar jihohin kudancin Kasar nan suna amfana da irin shiryen shiryen da Kamfanunuwa ke yi amma mu arewaci an barmu a baya.

Ya bada misali da bankuna inda yace duk banki da wuya a samu bahaushe Dan Asalin Jihar Kano ko Yan shara ba’a cika dauka ba, to wannan kungiya a shirye take don ganin ana sauke duk wannan nauyi.

Alhassan Haruna ya kuma ce wannan kungiya bata da alaka da siyasa ko bangaranci.
Kungiya ce kawai ta gwagwarmayar Kwato yancin Matasan jihar Kano.

Kuma idan tafiya tayi nisa za’a kafa Rassa a fadin kasar nan dama ketare kasancewar ko ina akwai yan jihar Kano, wayanda ake tauye musu hakkinsu ko muzguna musu musamman a yankin kudancin kasar nan.

Shima anasa Jawabin mai kaddamar da taken kungiya Dr Kabiru Sa’id Sufi ya nuna Farin cikin sa da Samar da wannan kungiya kasancewar irin su aka rasa a Arewacin Najeriya.

Ya kuma yabawa shugabannin irin yadda suke jajircewa da sadaukar da Dukiyoyinsu don ganin wannan kungiya ta zauna da kafarta.

Dr Sufi ya yaba musu matuka kasancewar kungiyar bata da alaka da siyasa ko bangarenci.

kuma a shirye yake wurin bada gudunmmawa a duk lokacin da aka Bukaci hakan daga garesu don dai samawa matasa hanyoyin dogaro da Kai.

Kungiyar ya samu halartar wakilan Kananan hukumomi daga

Dala, Fagge, Nassarwa, Tarauni, Kano Municipal, Dawakin kudu, da sauransu, har dama sauran mambobin kungiya, da suka halarci taron kaddamar da taken.

Leave a Reply

%d bloggers like this: