Gwamnatin jihar Borno ta soma maida mutanen da rikici tada kayar baya ya dai daita zuwa garuruwansu na asali.

Tare da gina masu muhallin su sakamakon yan kwarya- kwaryan zaman lafiya da aka soma samu a wasu kyauyuka.

Gwamnatin jihar dai tace ta gina sababbin gidaje guda dari biyar a kauyen Ajiri da wasu rukunin gidajen guda tamani a Auno a kananan hukumomin Mapa da Konduga da samar da ruwan sha a wadannan kauyuka da kayayyakin abinci.

ta kuma ce ta bada tallafin Naira dubu hamsin hamsin ga kowane magidanci da aka sake tsugunarwan.

Kwamishinan ma’ikatar gine gine da sake tsugunar da jama’a Injiniya Mustpha Gubiyo, shine ya bayyana hakan inda ya ce a yanzu haka akwai mutane sama da dubu biyu da aka riga aka tsugunar da su a wadannan kauyuka kuma gwamnatin ta tabbatar da an basu abubuwa da suke bukata na yau da kullum.

Ya ce gwamnatin jihar tana aikin hadin gwiwa da ma’ikatar ministan noma domin raba musu gonaki su fara aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: