Babban ofishin jakadancin Najeriya da ke Ottawa a kasar Canada ya sanar da rufe ofishin jakadanci da ke kasar.

Kazalika, ofishin jakadanci ya ce ya dakatar da duk wasu aiyuka da suka hada da aiyukan gaggawa a ofishin kamar yadda aka saba yi idan bukatar hakan ta taso.

Ofishin jakadancin ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne sakamakon harin da wasu batagari su ka kai ofishin jakadancin tare da raunata wasu ma’aikatan ofishin yayin neman sabunta fasfo.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin ya fitar ranar Laraba inda.

Sanarwar ta bayyana cewa, “babban ofishin jakadancin Najeriya a kasar Canada na sanar da ‘yan Najeriya mazauna kasar Canada da sauran jama’a cewa ta rufe ofishin jakadancin kasar.

“An dakatar da dukkan wasu aiyuka da suka hada da aiyukan gaggawa da ofishin kan yi idan bukatar hakan ta taso.

Leave a Reply

%d bloggers like this: