Gwamanan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya aike da saƙon taya murna ga ƴan jariya da Afrika a bisa nasarar yaƙar cutar polio a yankin.

cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar, Ganduje ya ce abin alfahari ne kuma abin jinjina ne ga kwamitin da ke jagorantar yaƙar cutar a Najeriya.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Ganduje ya yabawa shugabannin kwamitin da ke kula da aikin yaƙar cutar a jihar Kano, sannan ya yabawa gwamnatin shugaba Buhari a bisa yadda ta jajirce har aka samu nasarar yaƙar cutar.

An bayyana samun nasarar yaƙar cutar Poliyo a Afrika wanda a yanzu ta karɓi takardar shaidar yaƙar cutar a ƙasashen da ke cikinta.

Ko ya za a yi da cutar maleriya da ke tashe a jikin mutanen Najeriya? wannan wani batu ne mai zaman kansa wanda idan hali yayi za mu kawo muku rahoto a kai.