Connect with us

Addini

Rashin gyara ƴaƴa kafin aure na taka rawa wajen mutuwar aure – Malama Tasalla

Published

on

Cikin shirin Sirrin Ma’aurata da ake gabatarwa a Mujallar Matashiya a kafar sadarwa ta youtube.

Malama Fatima Nabulisi Baƙo wadda aka fi sani da Malam Tasalla, ta bayana cewar yana da matuƙar muhimmanci iyaye su maida hankali wajen kula da ƴaƴansu kafi su aurar da su.

Ta ce wannan babbar matsala ce da aka fi yawan samu wanda take taka rawa wajen sakin aure a yanzu

Ta ƙara da cewa, da yawan ma aurata na ƙorafin larura wanda iyaye baau cika maida hankali ko kulawa a kan abinda ke damun ƴaƴansu ba.

Duk da cewar ana samun kaɗan daga ciki masu kulawa da abinda ke damun ƴanƴansu, amma yawan waɗanda ba sa kulawar ya sa auren ke samun tangarɗa bayan an ɗaura.

Malama tsallah ta shawarci iyaye da su kasance masu sa ido tare da jan ƴanƴansu a jiki don jin abinda ke damunsu.

https://youtu.be/hMF6DRYPFLg

Click to comment

Leave a Reply

Addini

Malam AbdulJabbar Kabara Ya Kori Lauyoyin Sa Ya Buƙaci Kotu Ta Bashi Dama Zai Iya Kare Kansa

Published

on

Malam Abduljabbar Kabara ya ce ya kori lauyoyinsa saboda sun saɓa yarjejeniyar da suka yi.

Malamin ya bayyanawa kotun haka a yau Alhamis yayin da ake ci gaba da sauraron shari’ar.

A cewar malamin yanzu yana sake neman wasu lauyoyin da zasu tsaya masa.

Wannan shine karo na uku, da Malamin dake tsare a gidan gyara hali, ya sake watsi da Lauyoyinsa.

Malam Abduljabbar kamar yadda ya yiwa Lauyoyinsa na baya, yana zarginsu da gaza kare shi a gaban Kotu.

Su kuwa lauyoyin gwamnatin jihar Kano sun buƙaci kotun ta umurci hukumar dake baiwa marasa ƙarfi kariya a kotu kyauta, watau Legal Aid Council da ta bawa Malamin lauyan.

A ƙarshe, kotun ta amince da hakan kuma ta yi umarni ga Legal Aid Council ta bawa Abduljabar Lauyoyin da za su kare shi.

Sai dai, Malam AbdulJabbar ya buƙaci kotu ta rabu da shi zai iya cigaba da kare kansa, tunda duk lauyan da ya ɗauka sai ya ce ana yi masa barazana da rayuwarsa.

A ƙarshe mai shari’a ya ɗage zaman zuwa ranar 26 ga Mayu, 2022.

Continue Reading

Addini

Fasto Dake Sayar Da Aljanna Kan Kuɗi N310000, Ya Gurfana Gaban Mai Shari’a

Published

on

Ahmad Sulaiman Abdullahi

 

 

An gurfanar da Fasto Abraham malamin addini a kotu wanda ya faɗa ma mabiyansa cewa yana iya kai su aljannah, inda yace  musu Omuo-Ekiti ne ƙofar shiga aljanna.

Fasto Abraham dai ya nemi mabiyansa su biya kuɗi N310,000 domin shiga aljannah bayan ya ce masu ya san hanyar da ake bi a shige ta.

An gurfanar da faston a wata kotun majistare ta jihar Ekiti da ke zama a Ado-Ekiti.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Sufeto Johnson Okunade, ya ce laifin ya saɓa wa sashe na 416 na dokar laifuka ta jihar Ekiti na shekarar 2012.

Johnson ya ƙara da cewa kai Fasto Noah Abraham Adelegan a ranar 27 ga watan Afrilu, a Omuo Oke-Ekiti a yankin Omuo, ta hanyar karya da niyar zamba, ka gabatar da kanka ga taron jama’a a cocin Christ High Commission Ministry, Omuo, Oke-Ekiti, a matsayin wanda zai iya kaisu aljannah kafin tashin duniya.

Inda nan take suka biya kuɗi daga N300,000 zuwa N310,000 kwannensu.”

Lauyan wanda ake ƙara, Adunni Olanipekun, ya buƙaci kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa, inda ya ƙara da cewa a shirye yake ya gabatar da amintattun wadanda za su tsaya masa.

Sufeto Okunade yace bashi da ja akan buƙatar belin, amma ya buƙaci kotun da ta yi amfani da damar ta wajen bayar da belin ko kuma ƙin amincewa da shi.

Alkalin kotun mai shari’a Titilola Olaolorun ta bayar da belin wanda ake ƙara a kan kudi N100,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.

A ƙarshe mai shari’ar ta ɗage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Mayu.

Continue Reading

Addini

Hisbah A Kano Ta Cafke Ƴan Mata Takwas A Wajen Raƙashewa

Published

on

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sami nasarar kama wasu mata masu ƙananan shekaru a rukunin unguwar Nassarawa ta jihar.

Mai magana da yawun hukumar Lawal Ibrahim Fagge ya tabbatarwa da Matashiya TV cewar, an kama ƴan matan ne a wuraren hokewa kamar Pikolo Joint da wani gida mai suna ICU da ke unguwar Badawa a Kano.

Hukumar ta kai sumamen ne bayan samun rahooto a kan yadda ake samun ɓata gari na ta’ammali da miyagun kwayoyi da shan shisha da sauran ayyukan ashsha a wajen.

Babban kwamandan hukumar Ustaz Haroon Ibn Sina ya ja hankalin iyaye da su dinga kula da ƴaƴansu tare da tunatar da su a kan haƙkin da ya rataya a wuyansu na kula da tarbiyya.

Sa’annan ya aike da takardar gayyata ga iyayen ƴan matan da aka kama don ganin sun zo domin tantance yaran da aka kama.

Hukumar Hisbah ta ce ba za ta lamunci yadda wasu ɓata gari ke gudanar da ayyukan ashsha a jihar ba, kuma za ta sa ƙafar wando ɗaya da duk wanda ya yi ƙokarin tsallake dokokin ta.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: