Limamin masallacin juma a na usman bin fodio a unguwar Rimin kebe yayi jan hankali dangane da lalacewar shugabanci a Najeriya.

Mallam Zubair Muhammad Umar ya yi jan hankalin ne ganin zagayowar ranar samun yancin kai a najeriya.
Ya ce ya kamata shugabanni su kasance suna koyi da shugabannin farko wadanda suka karbi mulkin daga hannun turawa, ganin yadda suka kwatanta adalci ba tare da danne hakkin talakawansu ba.

Ya kara da cewa duba ga halin matsi da ake ciki a yanzu, ko ibada ba a samun ana yinta cikakkiya saboda fargaba daban daban, yace ya kamata mahukunta su duba halin da talakawa suke ciki na tsadar rayuwa, tare da samar da mafita wadda za ta kawo sauki ga al ummar Najeriya.
