Kungiyar Kwato Hakki da Sa-ido Kan Hana Rashawa da kididdiga(SERAP), ta maka Shugaba Muhammadu Buhari a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, inda ta nemi ta tilasta wa Shugaba Muhammadu Buhari bayyana sunayen wadanda gwamnatin sa ta kwato zunzurutun naira bilyan 800 daga hannun su.

A cewar kungiyar Buhari da bakin sa ya bayyana cewa gwamnatin sa ta “kwato naira bilyan 800 daga hannun barayin gwamnati.
Buhari ya yi wannan jawabi a cikin takardar da ya karanta, a ranar 12 Ga Yuni, ranar Dimokradiyya, inda ya kara da cewa, “Ana ci gaba da zuba kudaden cikin ayyukan raya kasa da gwamnati ke aikatawa.”

Cikin karar da SERAP ta shigar, ta nemi kotu ta tilasta Buhari ya bayyana sunayen barayin gwamnati da aka kwato naira bilyan 800 a hannun su.

Kazalika Shugaba Buhari ya bayyana naira nawa aka kwato ga kowane mutum daya.
Haka kuma kotun ta tilasta Shugaba Buhari ya bayyana ranakun da aka karbo ko nawa ne daga hannun kowane barawon gwamnati.
Serap ta bukaci kotu ta sanya Buhari ya fito ya bayyana dukkan ayyukan da ya ce an yi da kudaden da kuma inda aka yi ayyukan.
Sannan ya bayyana farashin da aka bayar da kowace kwangilar da aka biya a cikin kudaden.
SERAP ta ce ‘yan Najeriya na da hakkin sanin yadda aka yi da kudaden da kuma sanin barayin kasarnan , tare da sanin adadin naira nawa kowanen su ya sata.