Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jajantawa waɗanda iftila in ambaliyar ruwa ta yiwa ta’adi a Kano.

Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar.
Ya ce gwamna Ganduje ya yi addu ar Allah ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu a sanadin ambaliyar ruwan a Kano.

Yayin taron majalisar zartarwa na jihar Kano wanda ya gudana a Abuja, Ganduje ya ce lamarin ba iya iyalan waɗanda abin ya shafa bane kawaai, ya shafi dukkan al ummar jihar Kano.

Yayi addu ar Allah ya mayar da alherin abinda aka rasa a sanadin ambaliyar ruwan ta bana.