Talakawan Najeriya suna ƙaunar Buhari shi yasa nake so su haɗa kuɗi na yi masa sabuwar waƙa don bawa maraɗa kunya – Rarara

Fitaccen mawaƙinan Dauda Adamu wanda aka fi sani da Kahutu Rarara yaa bayyana dalilansa na neman karo karon talakawa don yiwa shugaban ƙasar Najeriya Buhari sabuwar waƙa.
A wata zantawa da mujallar Matashiya ta yi da mawaƙin ta wayar tarho, Rarara ya ce ana ta yaɗa farfaganda a kafafen sada zumunta cewar shugaban bashi da masoya, kumaa ya tabbata har yanzu shugaban yana nan a ran talakawa.

Ya ƙara da cewa da yawan masoyan shugaba Buhari basu da wayar da za au ɗora su wallafa a kafafen sada zumunta cewar suna nan daram ba gudu ba ja da baya.

Ya ce baya buƙatar wani sanata ko gwamnan ko wani mai kuɗi ya biya kuɗin waƙar, illa ƴan Najeriya da ya buƙaci kowanne ya tura naira dubu ɗaya don yin waƙar.
“Mun shirya zaƙulo manya manyan ayyuka a lungu da saƙo don sakawa a cikin waƙar,wanda hakan zai tabbatar da cewar Buhari yana aiki.
Anata yaɗa farfaganda Buhari ba ya aiki mu mun san aikin da yayi, amma ba za mu faɗa a sadaka ba” a cewar mawaƙin.
Da mujallar Matashiya ta tambayeshi shin ko zai cigaba da yin waƙar bayan an haɗa kuɗin a wannan karo? Rarara ya kada baki ya ce ” Ai waƙa yanzu aka fara, bama waƙa ba waƙoƙi kai” inji Rarara.
Muhawarar da aketa tafkawa kenan a kafafen sada zumunta a kan cewar mawaƙin ya buƙaci talakawa da su haɗa kuɗi don yiwa shugaban ƙasa sabuwar waƙa.
Rarara ya bayyana account ɗin da za a iya saka kuɗin kamar haka.
Banki Zenith Bank
Sunan Acoount ɗin Rarara Multimedia Nigeria Co.
Lambar Account ɗin 1016422103.