Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta yi holen masu aikata laifuka dabab daban  har mutane 36 a jihar.

Kwamishinan yan sandn jihar Olugbenga Adeyanju ne ya gabatar da masu laifin ga yan jaridu a harabar helkwatar rundunar.

Cikin mutanen  da aka kama akwai mutane goma sha takwas 18 da ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane, sai mutane 8 da ake zarginsu da aikata fashi da makami sannan mutane bakwai da ake zargi da aikata fyade sai mutum uku da ake zarginsu da satar motoci.

Rundunar ta yi nasarar kwato bindiga kirar AK47 guda uku tare da alburusai masu yawa, haka kuma ta kubutar da ababen hawa na mutanen da aka sace.

Bayan rundunar ta yi holen masu laifin sannan ta karrama wasu mutane da suke bawa rundunar gudunmawa wajen ganin an samar da tsaro a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: