Aƙalla mutane 340,089 ne suka kamu da cutar Korona a ƙasar saudiyya bayan samun sabbin mutane 474 da suka kamu da cutar a jiya talata.

Hukumar lafiya a ƙasar ta wallafa cewar an samu mutane 19 da cutar ta hallaka a jiya.
Cikin sanarwar da hukumar ta fitar ta ce mutane 326,339 ne suka warke daga cutar a fadin ƙasar sai mutane 5,087 da cutar ta yi ajali a faɗin ƙasar baki ɗaya.

A yanzxu haka dai mutane 8,663 ne ke ɗauke da cutar sai mutane 839 da suke cikin mawuyacin hali a sanadiyyar kamuwa da cutar.

Tuni aka fara komawa harkoki a ƙasar sakamakon shawo kan annobar cutar wadda ta yi sanadiyyar rufe wuraren ibada, kasuwanni, da wuraren wasanni.