Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bada shaidar kama aikin jagorancin kwamitin aikin AKK Gas ga Injiniya Mu’az Magaji Ɗan sarauniya.

A yayin da yake miƙa masa takardar jagorancin kwamitin, Ganduje ya ce an bashi damar ne bisa cancantarsa da jajircewarsa a kan aikin.
Mu’az Magaji wanda ke da kwarewar aiki a kamfanin mai natsawon shekaru, kuma ya fita ƙasashe da dama tare da gudanar da ayyuka daban daban kamar yadda ya bayyana a wani shiri da ya gabatar a Mujallar Matashiya.

Aikin zai taimaka wajen samar da aikin yi ga matasa a jihar Kano tare da kawo cigaba mai tarin yawa a jihar inji Ɗan sarauniya.

AKK Gas dai aiki ne da za a jawo iskar gas daga Ajakuta zuwa Kaduna zuwa Kano, kuma aiki ne na gwamnatintarayya.
Kafin kasancewarsa shugaban kwamitin Injiniya Dan sarauniya ya kasance kwamishininan ayyuka a jihar Kano kuma daga bisani aka saukeshi daga muƙamin.