Hukumar lura da tuƙi a jihar Kano Karota ta kama wani Ekennah Okechuku da ke safarar tabar wiwi mai tarin yawa

Hukumar ta miƙa motar da aka kama ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano.

A yayin da yake jawabin wajen miƙa tabar wiwi ga kwamandan hukumar NDLEA a kano Baffa Babba Ɗan Agundi y ace tuni suka samu umarnin tashin tashar manyan motoci da ke unguwar sabon gari wadda ake fakewa da ita ana aikata manyan laifuka.

Baffa Babba ya gargadi masu kamfanoni da su ja kunnen direbobinsu da cewar, muddin aka kama mota ɗauke da haramtaccen kaya gwamnatin jihar za ta kwace motar tare da rufe kamfanin da ya mallaki motar a jihar.

A yayin da yake jawabi shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyin a jihar Kano Dakta Ibrahim  Abdul ya ce a baya hukumarsu ta taɓa kama wanda ake zargi da safarar tabar wiwi, sannan ya jinjinawa hukumar ganin yadda suke taimaka musu wajen yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: