Wasu ƴan bindiga sun sace mutane goma sha tara a ƙauyen Kutunku da ke ƙaramar hukumar Wushishi ta jihar Neja.

Mutanen da aka sace waɗanda su ka haɗa da maza 11 sai mata 8 an sace su ne a safiyar yau Litinin.
Wani mazaunin garin y ace ƴan bindigan da su ka shiga garin sun fara harbin kai mai uwa da wabi ne sannan su ka tafi da mutanen.

Sannan ba su tuntuɓi iyalan waɗanda aka sace ba.

Daga cikin waɗanda aka sace akwai wasu amare guda biyu.
Har zuwa lokacin da muke kammala wannan labari ba mu samu jin ta bakin rundunar yan sandan jihar ba a kan lamarin.
Jihar Neja na a sahun gaba cikin jerin jihohin da ƴan bindiga su ka addaba a kwanakin nan.