Gwamnan jihar Kaduna ya sake jaddadda matsayar sa a kan ƙin biyan kudin fansa ga masu satar mutane da su ka addabi jihar Kaduna.

Gwamna Mallam Nasir El’rufa’I ya bayyana hakan ne a yayin zantawar sa da gida rediyo Najeriya Kaduna.

Gwamnan ya ce ko da ɗan sa aka kama ba zai biya kuɗin  fansa domin karɓo shi ba.

Malam Nasir El’rufa’I y ace ko da za a kashe ƴaƴan sa idan aka kama su ba zai biya kuɗi domin a karɓo su.

Sannan ya nuna takaicin sa a bisa yadda wasu ke tunanin bai damu da ɗaliban da aka sace ba a jihar sanadin rashin biyan kudin fansa.

Ya ce abin da yake gaban gwamnatin shi ne yadda za a kawo ƙarshen masu satar mutane a jihar baki ɗaya.

Tun a baya gwamnan Kaduna ke iƙirarin ƙin biyan kuɗin fansa ga ƴan bindiga domin a sako mutanen da su ke tsare da su.

Daga ƙarshe ma gwamnatin ta ce za ta hukunta duk wanda ya biya kuɗi ko yake tattauna wa da ƴan bindigan da sunan gwamnatin

Leave a Reply

%d bloggers like this: