Labarin da yake riskarmu a halin yanzu wani jirgin soji ɗauke da manyan sojoji ya yi hatsari ya yi sanadiyyar rasuwar shugaban sojin ƙasa na Najeriya Janar Attahiru.

Rahoton wanda Matashiya ba ta kai ga tabbatar da sahihancinsa ba ya nuna cewar babu wanda ya tsira daga cikin waɗanda suke cikin jirgin.
Jirgin ya yi hatsari ne da misalin ƙarfe shida na yammacin yau a filin sauka da tashin jirage na Kaduna.

Shugaban sojin da sauran manyan sojoji na cikin jirgin babu wamda ya tsira da ransa.

Har yanzu ba a kai ga gano sanadin hatsarin jirgin ba, sai dai an tabbatar da cewar an yi ruwan sama mai ƙarfi yayin da lamarin ya faru.
Cikakken labari na nan tafe…