Wasu matasa a kudancin Kaduna sun gudanar da zanga-zanga bisa kashe-kashe da ake yawan yi a yankin su.

Matasan ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar yankin sun ce ana yawan sace musu mutane da kuma kashe musu wasu ba tare da gwamnati ta ɗauki mataki a kai ba.
Matasan na ɗauke da kwalaye wanda su ka yi rubutu da ke nuna gazawar gwamnatin jihar.

Sannan sun buƙaci dukkan mahukuntan jihar da su tashi tsaye don fitar da iuta daga halin da take ciki.

A makon da muke ciki ne gwamntin jihar ta bayyana cewar daga watan Afrilun da ya gabata zuwa yanzu an kashe mutane 222 sannan aka sace wasu 774 sai kuma mutane 222 da aka illata.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren yan bindiga a cikin jihohin Arewacin Najeriya.