Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawo ƙarshen ƴan bindigan da su ka addabi ƙasar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun sa Femi Adesina ya fitar, ya ce harin da ƴan bindiga su ka kai makaranatar sojoji a Kaduna ya sa za a kawo ƙarahen su.
Ya ƙara da cewa jinin waɗanda a ka kashe ba zai tafi a banza ba.

Rundunar sojin Najeriyaa ta ce za ta ɗauki mataki a kan harin da a ka kai.

Kwana guda da kai harin, a ka ga gawar sojan da ƴan bindiga su kaa sace duk da cewar sun nemi kuɗin fansa naira miliyan 200.
A ranar Litinin wayewar Talata wasu ƴan bindiga su ka shiga makarantar sojoji ta NDA a Kaduna tare da kashe wasu biyu sannan au ka sace wani mai kukamin Manjo.