Kakakin ya ƙara da cewa daga ranar 12 ga watan Agustan da ya gabata zuwa ranar 1 ga watan Satumban da muke ciki akwai mayaƙan Boko Haram guda 5,890 da su ka miƙa wuya ga dakarun Operation Haɗin Kai.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta miƙa tubabbun mayaƙan Boko Haram 565 ga gwamnatin jihar Borno.
Kakakin hukumar Birgediya Janar Benard Onyeuko ne ya sanar da hakan a yayin taron manema labarai da ya gudana yau a Abuja.

Ya ce sun miƙa tubabbun mayaƙan ga gwamnatin Borno don ci gaba da matakin da ta shirya ɗauka a kan su.

Daga cikin mayaƙan da su ka mika wuya akwai kwamandojin su a ciki.
Sannan mayaƙan sun ajiye makamai masu yawa daga ciki akwai manyan bindigu ƙirar gida da na waje.
Sannan an samu nasarar cafke wasu mutane bakwai ke bai wa yan ta’adda bayanai kuma tuni su ka miƙa su wurin da ya dace don gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace a kan su.