Majalisar dattawa a Najeriya ta ce babu kudin da za a bai wa ƴan Najeriya mutane miliyan 40 naira 5,000 a matsayin rage raɗaɗin janye tallafin mai.

Kwamitin lura da ahrkokin kuɗi a majalisar ya ce kasafin da aka yi na shekarar 2022 ba zai bayar da damar da za a iya biyan yan kasar naira 5,000 a wata ba.

Shugaban kwamitin kuɗi a majalisar Sanata Adeola Olaminekan ne ya bayyana wa ƴan jarida haka jim kaɗan bayan ya gabatar da rahoton kwamitin sa a kan kasafin kudin shekarar 2022.

Ya ce babu wani ɓangare a kasafin wanda za a kalla don ware kuɗaɗen da za a biya ƴan ƙasar kuɗaɗen da gwamnatin ta ce za ta bayar.

Jimillar kuɗaden da ake tsammanin kashe wa a ɓangaren zai kai naira tiriliyan biyu da ɗigo hudu a wata.

Ya ƙara da cewa kafin tabbatar da hakan za a miƙa ƙudirin gaban majalisar kuma a nan ne za su ga inda za a zaƙulo kuɗaden da za a bai wa mutane.

Ministar kudi da kasafi a Najeriya ce ta bayyana cewar za a bai wa yan ƙasar tallafin naira dubu biyar domin rage musu raɗaɗin cire tallafin mai a ƙasar wanda za a yi a sabuwar shekarar 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: