Gwamna jihar Kano Dakta Abudllahi umar Ganduje ya ce rikicin cikin gida a jam’iyar APC ba zai ɗauke masa hankali a kan ayyukan ci gaba da gwamnatin sa ta sa a gaba ba.

A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Malam Abba Anwar ya fitar ranar Lahadi, gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wanda aka yi a fadar gwamnatin Kano.

Taron da aka yi wanda ya sami halartar sanatan Kano ta Kudu da ƴan majalisar tarayya 20 da ƴan majalisar jihar 28 sai shugabannin ƙananan hukumomi 44 da da shugabannin jam’iyya na mazaɓu da sauran su.

Ya ce faɗan cikin gida wani ƙaramin al’amari ne kuma ba zai sa su karkata a kan sa tare da sauka daga doron ayyukan ci gaba da gwamnatin sa ta sa a gaba ba.

Ya ce wannan al’amari ne da ya saba faruwa a cikin jam’iyya kuma al’ada ce ta demokaraɗiyya.

Mutanen da su ka halarta suns ake nuna goyon bayan su a kan tsarin tafiyar da gwamnati ƙarƙashin jagorancin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: