Daga Amina Tahir Muhammad Risqua

Gwamnatin tarayya ta fitar da ƙididdiga a kan yakin da take yi da ta’addanci a yankin Arewa maso gabashin kasar nan a shekarar da ake shirin ba bankwana da ita ta 2021, inda ta ce ta samu nasarar dkashe ‘yan tada kayar baya da dama.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, wanda ya yi
jawabi ga manema labarai a Legas, ya ce an kashe ‘yan ta’adda a Najeriya 1000.

Ya ce yayin da mahara 22,000 suka mika wuya, an ceto fararen hula 2000 a cikin shekarar da mu ke bankwana da ita.

Sannan akwai makamai da alburusai da aka kwato daga hannunƴan bindiga.
Lai Mohammed ya kara da cewa an lalata wasu masana’antun sarrafa bama-bamai na ISWAP da na Boko Haram.
A cewarsa, duk da kalubalen da ake fuskanta, sojojin sun samu nasarar cimma abin da ake bukata.
Ya ce “Musamman a shekara mai zuwa babban kalubalen shi ne na rashin tsaro. Duk da wannan kalubalen da aka saba fama da shi a fannin tattalin arziki.
“Rundunar tsaro ta Operation HADIN KAI ta kashe ‘yan ta’adda sama da 1000, an ceto fararen hula 2000 tare da mika wuya na ‘yan ta’adda sama da 22,000. harda iyalansu” a cewar sa.
Ministan ya ce an inganta aikin sojojin ne sakamakon jagorancin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da kuma jajircewar rundunar sojin kasar da shugabanninta.