Ƴan bindigan sun kai hare-haren ne cikin ƙauyuka 10 na jihar Zamafara sannan ake zargi sun hallaka sama da mutane 200 a ƙasa da awanni 48.

Rahotanni daga jihar Zamfara na tabbatar da cewar an gano gawarwakin mutane 143 na mutanen da ƴan bindiga su ka kashe a wasu hare-hare da su ka kai wasu ƙauyukan jihar.

An kai hare-haren ne a ranakin Laraba da Alhamis a ƙananan hukumomi Anka da Bukuyyum.

Rahotannin na cewar ko a jiya Juma’a sai da aka gano wasu gawarwaki da ƴan bindiga su ka kashe, sannan ana ci gaba da lalubo wasu gawarwakin a cikin dazukan ƙauyukan.

Wani mazaunin garin ya tabbatar da cewar an hallaka sama da mutane 200 wasu da dama an ƙone su da ransu a cikin gidajen su daga cikin mutanen da aka ƙone da ransu akwia mata da ƙananan yara.

Ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun tilasta wa mutanen zama a cikin gida sannan su ka banka wa gidajen wuta har su ka rasa rayukansu.

Ƙauyukan Rafin Danya, Barayar Zaki, Rafin Gero, Kurfa na daga cikin ƙauyukan da lamarin ya shafa.

Haka zalika wani da lamarin ya faru a gabansa wanda ya sha da kyar ya ce yan bindigan sun kore shanu da sauran dabbobi wadanda ba su gaza 3,000 ba.

Wani mai suna Malam Muhammad Sani ya ce har yanzu ƴan bindigan su na garin kuma sun hana yin jana’zar wasu da aka gano gawarwakin su a ƙauyen su.

Rundunar ƴan sandan jihar ta ce ta na ci gaba da bincike domin tattara bayanan alƙaluman mutanen da su ka rasa rayukansu a sanadiyyar hare-haren.

Leave a Reply

%d bloggers like this: