Daga Khadija Ahmad Tahir

Ala’amarin ya faru a wani gari a ƙaramar hukumar Taura ta jihar.

Rundunar ‘yan sandan jihar  Jigawa ta tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun hallaka jami’an ta su biyu tare da yin garkuwa da wani mutum a karamar hukumar Taura da ke Jihar.

Rundunar ta ce ‘yan bindigan sun hallaka su ne a lokacin da su ke kokarin kubutar da mutumin da ‘yan bindigan su ka yi garkuwa da shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Lawan Shisu shi ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labara na Najeriya NAN yau a Dutse babban birnin Jihar.

Ya kara da cewa zuwan ‘yan bindigan ke da wuya su ka shiga gidan wani dan kasuwa mai suna Alhaji Ma’aruf Abubakar inda nan ta ke su ka yi awon gaba da shi.

Shiisu ya ce ‘yan bindigan sun je ne da misalin karfe daya na dare kuma su ka tura jami’an su domin yakar ‘yan bindigan inda kuma jami’an su biyu su ka rasa rayukan su.

Ya ce sun aike jami’an dukkan lungu da sako domin cafko ‘yan bindigan tare kuma da kubtar da mutum da su ka yi garkuwa da shi.

Lawan shiisu ya bayyana cewa su na ci gaba da gudanar da bincike akan faruwar lamarin domin kawo karshe ‘yan bindigan a dukkan fadin Jihar.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: