Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ba ta da shirin janye tallafin man fetur a halin da ake ciki.

Ƙaramin minsitan man fetur a Najeriya Timipere Sylva ne ya sanar da haka ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari baya goyon bayan janye tallafin mai a ƙasar.

Minsitan ya bayyana haka a cikin wani shiri da aka gabatar da shi a gidan talabiji na Channels.

Ya ce gwamnatin ba ta da niyya ko goyon baya a kan batun janye tallafin mai da ake ta cece-ku-ce a kan sa.

A ƴan kwanakin nan ake raɗe-raɗin cewar gwamnatin na dab da ƙara farashin man fetur zuwa naira 302 maimakon 162 zuwa 165 da ake siyar da shi a halin yanzu.

Ko a makon da ya gabata, sai da ministan yaɗa labarai a Najeriya Lai Mohammed ya bayyana cewar, gwamnatin za ta tuntuɓi maus ruwa da tsaki a ɓangaren kafin zartar da hukunci.

Mutane da dama na kallon hakan a matsayin hanyar da za ta ƙara yawan matalauta a Najeriya ganin yadda  aka ta’allaƙa da man fetur wajen tafiyar da kasuwanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: