Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce jihar Osun da ke kudancin ƙasar ne ke da kaso mafi yawa na adadin mutanen da su ka yi rijistar katin zaɓe a yayin da ta yi nisa a zango na uku wajen yi wa mutane rijistar katin zaɓe.

A wani sanarwar da hukumar ta fitar a safiyar yau Talata bayan tattara alƙaluma a dangane da mutanen da su ka yi rijistar katin zaɓen, hukumar ta ce zuwa yanzu akwai mutane 8,919,606 waɗanda su ka aika da bayanansu domin yi musu rijistar katin zaɓe na din-din-din.
Bayan da hukumar ta tattara kuma ta fitar, ta ce matasa 5,528,085 ne su ka yi rijistar katin zaɓen, yayin da matsakaitan shekaru 2,252,249 su ka yi rijista, sai kuma wadanda su ka manyanta tsakanin shekaru 50-69 999,032 su ka yi rijistar, sannan tsofaffi 140,240 aka tabbatar sun aika bayanansu domin yi musu rijista.

Daga cikin jumillar mutanen da su ka yi rijsitar akwai 90,512 waɗanda masu buƙata ta musamman ne.

Sa’annan akwai ɗalibai, da ma’aikatan gwamnati da ƴan kasuwa waɗanda su ka aika da bayanansu domin mallakar katin zaɓe.
Hukumar ta ce a zango na uku da ta ke yi wa mutane rijitar katin zaɓen mutane 5, 353,744 aka yi wa rijistar zuwa yau Litinin.