Rundunar sojin Najeriya ta ce mayaƙan Boko Haram tsaye ISWAP su 104 sun miƙa kan su ga jami’an tsaro.

Mayakan da iyalansu 104 sun miƙa kansu tare da makaman da su ke dauke da su.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa, ta ce mayakan sun kai kansu ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata.

Ta kara da cewa daga cikin mayakan akwai maza 22 sai mata 27 sannan yara su 55.

Mayakan sun sun kai kansu ga runduna ta 25 da ke Damboa a jihar Borno.

A baya rundunar sojin ta ce mayaƙan sama da dubu ɗaya sun mika wuya tare da ajiye makamansu.

Tuni gwamnatin ta fara tunanin yadda za a mayar da mayakan su ci gaba da rayuwa a cikin jama’a.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: