A jihar Katsina kuma mutane shida ne su ka rasa rayukansu a yankin Shimfida da ke ƙaramar hukumar Jibia.

Hakan na zuwa ne yayin da aka janye jami’an tsaron da ke kula da yankin a ranar Laraba.

Mutane a yankin sun fara yin hijira zuwa wasu garuruwan domin steratar da rayuwarsu.

Shekaru bakwai jami’an soji su ka shafe a yankin bayan da aka taɓa kai wani mummunan hari yankin sai dai kuma an janye su a ranar Laraba.

Mutanen da aka kashe matasa ne da yara, kuma mutanen yankin sun koka a kan yadda aka janye jami’an sojin ba tare da sanar da su ba.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewar mata da maza manya da yara da tsofaffi sun tsere daga gidajensu bayan da aka wayi gari da gawar mutane shida.

Jami’an sojin ba su ce komai a dangane da janye jami’an a yankin ba, awanni ƙalilan aka samu tsakanin janye jami’an da kuma harin da aka kashe mutane shida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: