Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan a yau Juma’a.

Mahukunta a ƙasar sun tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan wanda hakan ya kawo ƙarshen watan Sha’aban a yau.
A Najeriya kuwa tun a jiya fadar sarkin musulmi ta bayar da umarnin fara duba jinjirin watan Ramadan a yau Juma’a.

Nan da wani lokaci za mu kawo muku rahoton yadda ta kasance a Najeriya.
