Maniyyata Aikin hajjin 1,105 a Jihar Gombe za su ziyarci kasar saudiyya domin sauke farali a aikin hajjin bana.

Babbar jami’ar hulda da jama’a ta hukumar jin dadin alhazai a jihar Hauwa Muhammad ce ta aikewa da manema labarai wasika bayan kammala taron wanda ta wakilci babban sakataren hukumar.

A cikin wasikar babban sakataren hukumar jindadin Alhazai na Jihar Sa’adu Hassan ne ya sanar da hakan a lokacin a yayin wani taro da hukumar ta shiryawa ma’aikatan hukumar.

A jawabin Sakataren ya bukaci maniyya aikin hajjin su kasan ce masu mayar da hankali a lokacin da su ka isa kasar ta saudiyya don gudanar da aikin hajjin.

Sakataren ya kuma yi kira ga ma’aikatan hukumar da kada su kasance masu cin zarafin maniyyatan,wanda hakan zai iya haifar wa da hukumar rashin ganin kimar ta a idanunun al’umma.

A cikin wasikar Sakataren ya kuma yi kira ga maniyyatan da su gujewa aikita laifuka wanda su ka sabawa doka ko safarar miyagun kwayoyi.

Sannan ya bawa gwanan Jihar sakamakon jajircewar da yayi wajen ganin ya nada kwararrun ma’aikita a hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: