Majalisar wakilai a Najeriya za ta binciki gudunmawar dala biliyan 1.777 da Najeriya ta baiwa kungiyar ƙasashen yammacin Afrika ta ECOWAS cikin shekaru 16.

A jiya ne majalisar ta bukaci kwamiti mai kula da harkokin majalisun dokoki da na majalisar ECOWAS da kuma harkokin kasashen waje da su bayyana alfanun gudummawar da kungiyar ta ECOWAS ta bayar wajen ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Najeriya a cikin shekaru 10 da suka gabata domin tantance gaskiyar al’amuran kasar.
Batun ya biyo bayan amincewa da kudirin da Awaji-inombek Abiante ya gabatar inda ya bayyana cewa a cikin shekaru 16, Najeriya ta bayar da gudunmawar dalar Amurka biliyan 1.177 ga kungiyar ECOWAS a matsayin harajin da ta dauka a tsakanin al’ummarta, yana mai cewa adadin shi ne mafi girman gudunmawar da kowace kasa ta samu tun kafuwarta.

Abiante ya ce, Najeriya ta bayar da gudummawa sosai ga samar don wutar lantarki ga ECOWAS ga kasashe mambobin kungiyar, ayyukan kiwon lafiya da kuma kokarin wanzar da zaman lafiya a kasashe mambobin da suka hada da Gambia, Mali, Saliyo, Guinea Bissau, Laberiya da sauransu.

Mataimakin shugaban majalisar Ahmed Idris Wase ya ce akwai ‘yan Najeriya da ke aiki da kungiyar ECOWAS a matsayin ma’aikatan wucin gadi, yayin da akwai wadanda suke aiki a can ba tare da karin girma ba sama da shekaru bakwai.