Shugaban Najeriya Muhammadu ya amince da fitar da naira biliyan 100 ga kamfanonin sarrafa magunguna na Najeriya.

Shugaban ya bayyana haka ne a yayin tarbar shugabannin ƙungiyar masu sarrafa magunguna ta ƙasa a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Shugaban ya ce bashin kuɗin da za a bai wa mutanen zai fita ne ƙarƙashin babban bankin Najeriya CBN ga ma aikatun sarrafa magunguna masu zaman kansu.

Bashin da za a bai wa kamfanonin za a basu ne ƙarƙashin shugaban kwamitin kuma mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Tsarin bayar da bashin an yi ne domin inganta fannin lafiya ta yadda za a habaka ɓangaren ta yadda za a ƙara musu ƙaimi don lura da ɓangaren.

Shugaban ya yabawa kamfanonin da ke samar da magunguna musamman yadda su ka taka rawa lokacin annobar Korona, da ɓangaren masu larurar tari, da shawo kan zazzaɓin cizon sauro har ma sa masu larurar cuta mai karya garkuwar jiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: