Majalisar wakilai ta gayyaci ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Hajiya Zainab Ahmed domin ta gabatar da dukkan takardun da suka shafi batun tallafin mai daga 2013 zuwa yau.

Ibrahim Aliyu, shugaban kwamitin wucin gadi na musamman da ke binciken tsarin tallafin man fetur ne ya bayyana hakan a lokacin da Stephen Okon, Daraktan kudi na cikin gida a ma’aikatar ya bayyana a gabansa a Abuja yau Talata.
Shugaban kwamitin ya baiwa ministar zuwa ranar 16 ga watan Agusta ta kawo kanta da duk wasu takardun da suka dace a ikirarin tallafin man fetur.

Shugaban ya ce dole ne ministar ta amsa tambayoy kan jimillar kudaden da aka fitar daga asusun ajiyar kudaden shiga a matsayin na tallafin Mai daga 2013 zuwa yau.

Ya ce dole ne a gabatar da bayanan kamfanonin da suka ci gajiyar kudaden tallafin daga asusun tattara kudaden shiga.
A cewar shugaban, furucin da ministar ta yi kwanan nan na cewa kasar za ta bukaci Naira tiriliyan 6.7 na tallafin man fetur abin damuwa ne ainun.
Ya ce ya zama wajibi ministar ta gurfana a gaban kwamitin domin bayyana wasu batutuwa, inda ya ce tun da za a aro kudin tallafin ne domin ‘yan Najeriya su mora.