Hukumomin tsaro a babban birnin tarayya Abuja sun kama mutane 480 wadanda ake zargi sun tsere daga gidan yarin kuje a yayi harin ‘yan bindiga.

Shugaban jami’an tsaron karta kwana a birnin Mista Beenet Igwe shine ya tabbata da kama mutanen.
Igwe ya bayyana cewa mutanen da aka kama su na boyewa ne a wasu gine-gine da ba a gama ginawa ba da ke unguwar maitama da wuse ll a Abuja.

Bayan kamo mutanen sun bayyana cewa sun samu mafaka ne a cikin gine-gine da ba a gama ba a cikin birnin na Abuja tare da aikata laifuka domin kaucewa kamun jami’an tsaro.

Igwe ya ce an kama mutanen ne dauke da makamai da su ka hada da Layu Wayoyin salula bindugu adduna kayan ‘yan sanda da sauran wasu kayyakin aikata laifuka.
Mista Igwe ya ce daga cikin mutanen da su ka kama ya na kyautata zaton wasu sun tsere ne daga gidan yarin kuje.
Shugaban ya ce a yunkurin da su ke na kamo masu laifi za su shiga cikin kauyuka 21 na Gishiri Kabusa wasa Waru da sauran wasu kauyukan da ke birnin na Abuja.
Igwe ya bayyana cewa za su zurfafa bincike akan su domin tantancewa.