Kimanin mutum 51 da ake sace a yankin Millenium City da ke Jihar Kaduna sun shaki iskar ’yanci bayan shafe makonni a hannun ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su.

Mazaunan Unguwar Keke B 35 da kuma na Unguwar Sabon Gero 16 da ’yan bindigar suka sace sun dawo matsugunansu ne a yau Asabar.

Bayanai sun ce jama’ar Unguwar Keke B 35 da aka sace sai da suka biya kudin fansa na naira miliyan 2 gabanin su kubuta.

Sai dai Daily Trust ta ruwaito cewa, babu wata fansa da aka biya gabanin sako mazauna Unguwar Sabon Gero 16 kamar yadda jagoran rundunar hadin gwiwa da ke yankin, Uwasu Yunusa ya tabbatar.

Haka kuma, wani jagoran al’umma da ke Unguwar Keke B da ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da biyan fansar naira miliyan biyu da mutanensa suka yi gabanin su shaki iskar ’yanci.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a karshen watan Yulin da ya gabata ne maharan suka far wa unguwar Keke B misalin karfe 9.00 na dare suna shiga gidaje su tisa keyar mutane zuwa cikin daji.

Wani mazaunin unguwar Keke A da ya zanta da wakilin Daily Trust a lokacin faruwar lamarin, ya ce cikin wadanda aka sace har da surukarsa da wasu ma’aurata da dansu na goye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: