Jami’an tsaro a jihar Kaduna sun kai samame maboyar rikakken ‘dan bindiga Lawan Kwalba a karamar hukumar Chikun ta jihar inda suka samo kayayyakin hada bama-bamai.

Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida, Samuel Aruwan, yace jami’an tsaron sun samo buhunan taki 27 wadanda ake amfani da su wurin hada abubuwa masu fashewa a cikin dajin Chikun.
Aruwan yace, dakarun sun kakkabe sansanin Kwalba dake Fadin Dawa a yankin Dende na karamar hukumar a jiya Alhamis.

Jami’in gwamnatin yace jami’an tsaron na matukar kokari kan yadda suka zage-damtse wurin yaki da ta’addanci a jihar.

Aruwan yace a bayanai da gwamnatin jihar ke samu, dakarun Operation Forest Sanity sun yi aikin ne bayan samun bayanan sirri a kan ƴan bindigan.